Matsin Lambar Yahudawan Sahayoniyya Kan Majalisar Dinkin Duniya
Matsin lambar yahudawan sahayoniyya da kawayensu na kasashen yammacin Turai ya tilasta wa Majalisar Dinkin Duniya janyewa daga kan matsayinta.
Ci gaba da yin watsi da hakkokin al'ummar Palasdinu da Majalisar Dinkin Duniya ke yi a tsawon tarihi, a wannan karo ya gamu da kalubalen babbar jami'ar gudanarwa a kwamitin kula da harkar tattalin arziki da zamantakewa a yankin yammacin Asiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya {ESCWA} a takaice.
A cikin 'yan kwanakin nan ne babbar jami'ar gudanarwa a kwamitin kula da harkar tattalin arziki da zamantakewa a yankin yammacin Asiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya {ESCWA} a takaice Rima Khalaf ta fitar da rahoton cewa:Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana ci gaba da gudanar da bakar siyasar cin zarafi da nuna wariya kan al'ummar Palasdinu musamman a yankunan Palasdinawa da ta mamaye. Wannan rahoto ya yi tsananin bakanta ran gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da na kwayenta musamman kasar Amurka, sakamakon haka mahukuntan haramtacciyar kasar ta Isra'ila suka dauki matakin yin kakkausar suka kan Majalisar Dinkin Duniya tare da bayyana rahoton a matsayin nuna kiyayya ga yahudawa kamar yadda ya faru a kasar Jamus a lokacin Hitler, Ita kuma tawagar kasar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta zaburo da karfinta ta hanyar yin kakkausar suka kan rahoton.
Bayan matakan matsin lamba da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kawayenta suka dauka kan Majalisar Dinkin Duniya tare da yin dirar mikiya kan rahoton, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kawar da rahoton amma Rima Khalaf taki mika wuya ga wannan bakar siyasa, don haka alatilas ta yi murabus daga kan mukaminta na babbar jami'ar gudanarwa a kwamitin kula da harkar tattalin arziki da zamantakewa a yankin yammacin Asiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya {ESCWA} a takaice.
Yana ci gaba da bayyana a fili cewa; Duk wani jami'in kasa da kasa musamman Majalisar Dinkin Duniya da ya lashi takwabin fayyace gaskiya kan bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, to dole ne ya shirya wa daukan matakin sadaukar da aikinsa kamar yadda ya faru ga Rima Khalaf. Sakamakon haka mafi yawan rahotonnin da ake fitarwa kan matsalar Palasdinu musamman na bangaren Majalisar Dinkin Duniya ake rufe ido kan bakar siyasar zaluncin yahudawan sahayoniyya tare da nuna wariya kan al'ummar Palasdinu musamman mazauna yankunan da suke karkashin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.