Yunkurin Dakile Kwararar Bakin Haure Daga Libya
(last modified Mon, 20 Mar 2017 17:59:48 GMT )
Mar 20, 2017 17:59 UTC
  • Yunkurin Dakile Kwararar Bakin Haure Daga Libya

Ministocin harkokin cikin gida na kasashen gungun tuntuba a tekun bahar Rum sun yi wata ganawa yau Litini domin tattauna hanyoyin dakile kwararar bakin haure tun daga Libya.

Shekara guda bayan cimma wata yarjejeniya da Turkiya don dakile kwararar bakin haure zuwa Girka, kungiyar tarayya Turai na son cimma matsaya irin wannan da Libya.

Don haka a cewar wata gajeriyar sanarwa da wakilan kasashen suka sanyawa hannu yau a birnin Rome na Italiya sun ce zasu maida hanakali wajen hadin gwiwa domin tunkarar matsalar.

 Kasashen dai sun hada da Italiya, faransa, Jamus Autrish, Slovakia, Suiziland da Malta ta bangaren nahiyar Turai, sai kuma bangaren Afrika Tunusia da kasar Libiya wace shugaban gwamnatin ta Fayez al-Sarraj, ya halarci ganawar.

A baya bayan dai samun yanayi mai kyawo ya taimaka sosai wajen ci gaba da kwararar bakin haure inda ko a ranar lahadi data gabata kimanin mutane 3,000 ne aka ceto daga Tekun Bahar Rum a gabar ruwa ta kasar Libiya a cewar dakaraun tsaro gabar ruwa na Italiya.