Faransa Ta Yi Kashedi Akan Rage Karfin Tawagar MONUSCO
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18714-faransa_ta_yi_kashedi_akan_rage_karfin_tawagar_monusco
Faransa ta yi kashedi akan duk wani yunkuri na rage yawan dakarun tawagar wanzar da zamen lafiya ta MDD a Jamhuriya Demukuradiyyar Congo.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 22, 2017 00:51 UTC
  • Faransa Ta Yi Kashedi Akan Rage Karfin Tawagar MONUSCO

Faransa ta yi kashedi akan duk wani yunkuri na rage yawan dakarun tawagar wanzar da zamen lafiya ta MDD a Jamhuriya Demukuradiyyar Congo.

Matakin sabunta aikin tawagar MONUSCO a wannan kasa ta R D. Congo na bukatar amuncewar sabuwar gwamnatin Amurka wace ke son rage tallafin da take bayarwa ga shirin wanzarda zamen lafiya na MDD.

Jakadan faransa a MDD, François Delattre ya ce rage karfin tawagar a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da babban zabenta cikin wannan shekara babban hadari ne. 

Amurka dai na samar da kashi 29% na kasafin kudade Milyan 7,9 na Amurka da ake warewa aikin tawagar ta MDD data kunshi dakaru 19,000 a R.D Congo.

A halin da ake ciki dai babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, ya bukaci kwamitin tsaro da ya kara karfin aikin tawagar ta MONUSCO da 'yan sanda 320, da kuma rike yawan dakarun soji da ake dasu a kasar ta R.D Congo.