Majalisar Musulmin Birtaniya Ta Yi Allawadai Da Harin London
(last modified Sat, 25 Mar 2017 06:45:18 GMT )
Mar 25, 2017 06:45 UTC
  • Majalisar Musulmin Birtaniya Ta Yi Allawadai Da Harin London

Musulmin kasar Birtaniya sun yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin London.

Jaridar Guardian ta habarta cewa, babbar majalisar musulmin kasar Birtaniya Muslim Council of Brotain MCB ta fitar da bayani da ke yin Allawadai da kakkausar murya kan harin da aka kai kan jama’a abirnin London.

Harun Khan shi ne babban sakataren majalisar musulmin kasar ta Birtaniya ya bayyana cewa, suna yin Allawadai da wannan hari, bayan haka kuma suna tabbatar wa duniya da cewa ba shi da wata alaka da addinin muslunci.

Sadiq Khan shi ne magajin garin birnin London kuma musulmi, ya bayyana cewa abin ya faru ko shakka babu aiki ne na ta’addanci, kuma dole ne kowa ya yi Allawadai da hakan, amma kuma a lokaci guda hakan ba zaitaba zama dalili na kyamar musulmi ba, saboda wasu da ke kiran kansu musulmi sun aikata ta’addanci domin kashin kansu, domin kuwa ba suna wakiltar muslunci ba ne a lokacin da suka aikata ta’addanci.