Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Bukatar Raba Duniya Da Makaman Nukiliya
Mataimakin shugaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada bukatar ganin an kawo karshen duk wani makamin nukiliya a duniya.
A jawabin da ya gabatar a jiya Litinin mataimakin shugaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya Mas'ud bin Mu'umin ya bayyana cewa: Shekaru kimanin 70 ke nan Majalisar Dinkin Duniya tana kokarin ganin an kawo karshen duk wani makamin kare dangi musamman makamin nukiliya amma har yanzu babu wani kwakkwaran matakin da kasashen da suka mallaki makaman suka dauka da nufin aiwatar da wannan bukata.
Mas'ud bin Mu'umin ya kara da cewa: Idan aka yi la'akari kan irin makuden kudaden da ake kashewa wjen kera makamin nukiliyar, ci gaba da kula da shi gami da kara karfafa shi, ba karamin makuden kudade ake kashewa ba, sakamakon haka da za a yi amfani da wadannan kudaden wajen gudanar da ayyukan bunkasa ci gaban kasa da kyautata rayuwar bil-Adama da hakan ya fi zama mai amfani ga duniya baki daya.
Tun a jiya Litinin ne aka bude zaman taron tattauna batun hana kera makaman nukiliya a duniya a birnin New York na kasar Amurka amma manyan kasashen da suka mallaki makaman na nukiliya ba su halacci zaman taron ba musamman wakilan kasar Amurka, Rasha, Faransa da kuma Italiya.