Gwamnatin Myanmar Ta Rusa Sansanonin Tsugunnar Da Musulmi
Gwamnatin Myanmar ta rufe manyan sansanoni guda uku da aka tsugunnar da dubban daruruwan musulmi ‘yan kabilar Rohingya.
Kamfanin dillancin labarai na shafqna cewa, rundunar sojin kasar Mayanmar tare da umarnin gwamnatin kasar ta rufe sansanonin da aka tsugunnar da musulmi a cikinsu.
Wannan mataki na mahukuntan kasar Myanmar ya zo ne bayan rahoton da kwamitin majalisar dinkin duniya karkashin jagorancin tsohon babban sakataren majalisar Kofi Annan, da ke bin kadun hakikanin abin da ya faru da musulmin Mayanmar ya bayar, da ke nuni da irin mawuyacin halin da musulmin kabilar Rohingya suke ciki a wadannan sansanoni.
A kwanakin baya ne kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya zargi rundunar sojin Myanmar da tafka laifukan yaki, ta hanyar yin kisan kiyashi a kan musulmin kasar.
Kwamitin dai ya dogara da rahotannin da kwamitin Kofi Annan ya gabatar, da sauran rahotanni da kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, kan cin zarafi da kisan kiyashi da sojin gwamnatin Mayanmar da kuma mabiya addinin buda masu tsatsauran ra’ayi suke yi a kan musulmi.