Sharhi : Yadda Erdogan Ya Sha Da Kyar A Zaben Raba Gardama
Bisa sakamakon kidayar kuri'un da aka jefa da kamfanin dillancin labaru na Anadolu na kasar Turkiya ya gabatar an ce, a zaben jin ra'ayoyin jama'a da aka yi a kasar, kimanin kashi 51.35 % sun amince da a kawo gyara ga kundin tsarin mulkin kasar.
Ita ma a sakamakon data bayar hukumar koli mai kula da zabe ta kasar (YSK) ta tabbatar da makamancin wannan sakamakon wanda ta ce ya samu amuncewa da 'ar tazara kadan da masu adawa da shirin gwamnatin kasar.
A cewar hukumar zaben ya samu karbuwa da kashi 85% na kimanin al'ummar kasar miliyan 55,3 wadanda suka tantanci kada kuri'ar.
Saidai a zaben da aka gudanar shugaba Erdogan ya sha da kyar a galibin mayan biranen kasar da suka hada da Satanbul, Ankara da kuma Izmir inda masu adawa da shirin suka fi rinjaye.
Ko ga baya ga hakan jihohion kudu maso gabashin kasar inda Kurdawa suka fi rinjaye sunyi watsi da shirin da zai baiwa shugaban kasar cikaken karfin iko.
Duk da cewa Erdogan ya yi nasara a zaben, babban koma baya ne garesa akan yadda akayi watsi da shirin a birnin Satanbul dake zama tushen fara shiga fagen siyasarsa a cewar Soner Cagaptay, wani masanin harkokin siyasar Turkiyyar.
A bayyanin da yayi a gidan talabijin din kasar Shugaba Erdogan ya jinjina akan abunda ya kira na farko a cikin tarihi ga al'ummar Turkiyya tare da kira ga kasashen duniya dasu amunce dasu mutunta sakamakon zaben.
Shugaban wanda ya sha da kyar a zaben ya kuma bukaci wani zaben jin ra'ayin al'ummar kasar akan dawo da dokar hukuncin kisa, lamarin da zai kasance babban kalubale ga kasar dake fatan zama mamba a kungiyar tarayya turai (EU)
Zaben jin ra'ayoyin jama'a kasar dai da aka yi, ya shafi kawo gyara ga wasu ayoyin doka na kundin tsarin mulki, ciki har da kudurin canja tsarin kasar daga tsarin majalisar dokoki zuwa tsarin shugaba wanda shi ne ya fi jawo hankali sosai.
Bisa daftarin gyara kundin tsarin mulkin kasar, za a kafa mukamin mataimakin shugaba guda biyu, kana shugaban kasar zai iya nada mataimakin shugaba da ministocin gwamnatin kasar, kana shugaban kasar zai iya ci gaba da zama shugaban jam'iyyarsa.
Akwai kuma batun soke mukamin firaministan kasar, sai kuma batun kara baiwa shugaban kasar iko a cikin kundin tsarin mulkin kasar da za a gyara.
Kundin zaben ya nuna cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa ranar 3 ga Nuwamban 2019, kana kuma shugaban da za'a zaba zai yi wa'adin mulki shekara biyar har sau biyu.
A halin da ake ciki hukumar zaben kasar na da mako guda domin ta gabatar da sakamakon kidaya kuri'un a hukumance.
Yanzu haka dai shugaba Erdogan zai iya tsayawa takara har sau biyu da za ta ba shi damar ci gaba da kasancewa kan karagar mulki har zuwa shekara 2029.
Tuni dai mayan jam'iyyun adawa na kasar da suka hada da CHP da HDP ta Kurdawa suka kalubalanci sakamakon zaben wanda suka ce yana cike da magudi da kura-kurai tare da shan alwashin shiga da kara.
Kungiyar tarayya turai dake takun tsaka a baya bayan da kasar ta Turkiyya ta bukaci hadin kan al'ummar kasar tare da kira ga gwamnatin kasar data yi taka tsantsan a matakai na nan gaba.