Masu Addinin Buda Sun Lakada Wa Malaman Musulmi Duka A Myanmar
(last modified Tue, 18 Apr 2017 06:28:17 GMT )
Apr 18, 2017 06:28 UTC
  • Masu Addinin Buda Sun Lakada Wa Malaman Musulmi Duka A Myanmar

Wasu masu tsatsauran ra’ayin addinin Buda sun lakada wa wasu malaman addinin muslunci ‘yan kabilar Rohingya duka a kasar Myanmar.

Kamfanin dillancin labaran arakan cewa, shugabannin addinin Buda a yankin Rakhin na kasar Myanmar, sun sanya mabiyansu sun lakada wa wasu malaman musulmi duka, bisa hujjar cewa ba su biya harajin da aka dora musu ba.

Shugabannin addinin Buda a yankunan Badang da kuma Shagur, sun dora wa malaman musulmi haraji, matukar suna son su koyar da karatun addinin muslunci ko kuma gudanar da sallar Juma’a a masallatansu.

Shugabannin addinin Buda sun ci zarafin manyan malamai biyu na musulmi a cikin wadannan yankuna, bisa hujjar cewa ba su biya harajin da aka dora musu ba.

Wanann haraji dai ba shi da wata alaka da gwamnati, amma kuma gwamnatin kasar ta Myanmar ba ta hana shugabannin addinin Buda karbar wanann haraji da musulmi ba, kamar yadda ake cin zarafin malamai da dalibai a gaban jami’an tsaro, matukar dai suka yi jinkirin biyan harajin da ‘yan addinin Buda suka dora musu.