Austria: An Dakatar Da Batun Shigar Turkiya A Cikin Tarayyar Turai
(last modified Tue, 18 Apr 2017 06:28:52 GMT )
Apr 18, 2017 06:28 UTC
  • Austria: An Dakatar Da Batun Shigar Turkiya A Cikin Tarayyar Turai

Gwamnatin kasar Austria ta sanar da cewa, an dakatar da duk wata tattaunawa kan batun shigar kasar Turkiya a cikin kungiyar tarayyar turai.

Shugaban kasar Austria Alexander Van der Bellen ne ya bayyana hakan a jiya, inda ya ce kuri'ar raba gardamar da aka gudanar a kasar Turkiya ta sanya kasar ta kara nisa matuka da tafarkin dimukradiyya, wanda hakan ya kara nisantar da kasar daga mafarkin shiga cikin tarayyar turai.

A nata bangaren shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Markel ta bayyana cewa, sakamakon kuri'ar raba gardama da aka kada a Turkiya, ya nuna cewa kan al'ummar kasar a rabe yake.

Kimanin kashi 51.3 na kuri'un da aka kada ne suka amince da karawa Erdogan karfin iko.