Venezuela : Maduro Ya Bukaci A Tuhumi Kakakin Majalisa Kan Juyin Mulki
(last modified Wed, 19 Apr 2017 05:22:39 GMT )
Apr 19, 2017 05:22 UTC
  • Venezuela : Maduro Ya Bukaci A Tuhumi Kakakin Majalisa Kan Juyin Mulki

Shugaba Nikolas Maduro na Venezuela ya bukaci da a tuhumi shugaban majalisar dokokin kasar kan kiran juyin mulki ga gwamnatinsa.

Mista Maduro ya bayyana cewa kiran da Julio Borges ya yi na cewa kada su bi umurninsa tamakar kiran juyin mulki ne ga gwamnatinsa.

Shi dai shugaban majalisar dokokin kasar Julio Borges, ya bukaci sojojin kasar dasu yi biyaya ga kundin tsarin mulki ta hanyar barin 'yan adawa su gudanar da zanga-zangarsu cikin lumana.

Yau kusan makwani uku kenan da 'yan adawa a wannan kasa ke gudanar da zanga-zanga inda yanzu haka mutane biyar ne aka rawaito cewa sun hallaka a yayin arangama da jami'an tsaro, kana kuma ana tsare da sama da wasu 200.

A wani abu kuma da ake ganin zai iya jefa kasar cikin wani sabon rikici yau Laraba ne bangaren 'yan adawa da masu mulki suka kira magoyan bayansu dasu fito wata zanga-zanga gama gari.