An Amince Da Dokar Koyar Da Kur'ani A Makarantun Pakistan
Majalisar dokokin kasar Pakistan ta amince da dokar da ke wajabta koyar da karatun kur'ani mai tsarki a dukkanin makarantun firamare da sakandare na kasar.
A zaman da majalisar dokokin kasar ta Pakistan ta gudanar a jiya, ta kada kuri'a a kan wannan dafrin kudiri, wanda dukkanin 'yan majlaisar suka amince da shi.
Wannan doka dai na nufin saka koyar da karatun kur'ani mai tsarki ya zama wajibi a dukkanin makarantun kasar Pakistan na gwamnati da kuma masu zaman kansu, dokar ta ayyana koyar da karatu ga daliban makarantun firamare daga aji na daya zuwa a ji na shida, kamar yadda kuma dokar ta wajabta koyar da karatu da kuma ma'anonin ayoyin kur'ani ga daliban makarantun sakandare, daga aji na daya har zuwa shida.
Tun a shekarar da ta gabata ce a agabatar da wannan daftarin kudiri a gaban majalisar dokokin Pakistan, amma an jikirta kada a kuri'a a kansa ne domin yi shawara da sauran gundumomin kasar, gami da malaman addini da kuma shugabannin kabilun kasar, wadanda dukakninsu suka amince da hakan.