Taho Mu Gama Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Adawa A Venezuela
(last modified Fri, 21 Apr 2017 05:34:03 GMT )
Apr 21, 2017 05:34 UTC
  • Taho Mu Gama Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Adawa A Venezuela

'Yan Adawan Gwamnatin Venezuela sun yi arangama da jami'an 'yan sanda yayin da suke ci gaba da zanga-zangar ganin bayan milki Nicolas Maduro a jiya Alkhamis

‘Yan Adawa a Venezuela sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga da za ta kifar da gwamnatin Nicolas Maduro duk da hasarar rayuka biyu da aka samu a arangama da suka yi da ‘yan sanda a ranar Laraba.

Rahotanni sun ce an kashe wani matashi mai shekaru 17 da wata mata mai shekaru 23 a gagarumar zanga-zangar da aka kaddamar a ranar Larabar da ta gabata. Sannan an hallaka wani soja a wajen Caracas, abin da ya kawo adadin mutanen da aka kashe yanzu zuwa 8.

‘Yan Sandan kwantar da tarzoma sun harba hayaki mai sa hawaye kan matasan da ke jifar su da duwatsu,zanga-zangar ta adawa ta bazu daga  Caracas babban birnin kasar zuwa sassan Venezuela.

A bangare kuma kuma  akwai magoya bayan shugaba Nicolas Maduro da suka gudanar da zanga zangar nuna goyon baya ga shugaban da ya gaji Hugo Chavez.

Tun a Shekarar 2014 Maduro ke fuskantar bore a Venezuela musamman kan adawa da tabarbarewar tattalin arzikin kasar mai dogaro da arikin fetir.