Viladimir Putin Ya Jaddada Wajabcin Daukan Matakan Yaki Da Ta'addanci
Shugaban kasar Rasha ya jaddada wajabcin samun ingantacciyar mahanga a fagen yaki da ta'addanci.
A jawabinsa a zaman taron kasa da kasa kan tsaro karo na shida a birnin Moscow a jiya Laraba: Shugaban kasar Rasha Viladimir Putin ya bayyana cewa matakin yaki da ta'addanci musamman a yankin gabas ta tsakiya da yankin arewacin Afrika yana bukatar samun ingantacciyar mahanga domin samun nasararsa.
Putin ya kara da cewa: Gudanar da tattaunawa da musayar mahanga a tsakanin mahalatta zaman taron kasa da kasa kan tsaro na birnin Moscow dangane da matsalolin tsaro da suke ci gaba da addabar duniya sune manyan batutuwan da za a fi maida hankali kansu a zaman taron.
A jiya Laraba ce aka bude zaman taron kasa da kasa kan tsaro karo na shida a birnin Moscow na kasar Rasha kuma kasashe kimanin 80 na duniya ne suka samu halatta.