Duban 'Yan Gudun Hijra Ne Aka Mayar Gidajensu A Kasar Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/world-i199-duban_'yan_gudun_hijra_ne_aka_mayar_gidajensu_a_kasar_iraki
Ma'aikatar dake kula da 'yan gudun hijra ta Kasar Iraki ta sanar da mayar duban 'yan kasar gidajen su.
(last modified 2018-08-22T06:57:45+00:00 )
Feb 02, 2016 14:05 UTC
  • Duban 'Yan Gudun Hijra Ne Aka Mayar Gidajensu A Kasar Iraki

Ma'aikatar dake kula da 'yan gudun hijra ta Kasar Iraki ta sanar da mayar duban 'yan kasar gidajen su.

A wata sanarwa da ya fitar yau Talata, Hamudi Mahjub daya daga cikin shugabanin ma'aikatar dake kula da 'yan gudun hijra na kasar Iraki ya ce A halin yanzu iyalai dubu 97 da 500 ne wadanda matsalar t'addanci ya bara da gidajensu aka mayar da su yankunan su dake jahohin Diyala, Silahuddin, da kuma Anbar.

Hamudi Mahjub ya kara da cewa tun a shekara 2014, ma'aikatar su ta bukaci dukkanin ma'aikatun dake dukkanin jahohin kasar da su yi rajistar dukkanin iyalan da matsalar ta'addanci ya raba su da mahalinsu.

Magabatan galgajiya na jihar Diyala sun sanar da komawar iyalai kimanin 200 gidajensu dake yankin Jula na Jihar.

Sama da wattani 7 kenan da kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ta mamaye wasu yankunan kasashen Iraki da Siriya, a tsakanin wannan lokaci, 'yan ta'addar na Da'esh ko kuma ISIS sun yi ta'addanci irin daban-daban inda suka kashe dariruwan mutane tare da yin sanadiyar raba wasu duban irakiyawa da gidanjensu.