An Bada Umurnin Yi Wa Kudin Tsarin Mulkin Kasar Venezuela Gyara
Shugaban kasar Venezuela Nikola Madoros ya rattaba hannu a kan umurnin gudanar da zabe da kuma samar da sabuwar majalisa wacce take da ikon sauya kundin tsarin mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Spanish news agency EFE ya bada labarin cewa shugaban kasar Venezuela Nikolas Masoro ya bukaci a gydanar da sabon zaben majalisar dokokin kasar, majalisa wacce take da damar gabatar da sauye sauye a cikin kundin tsarin mulkin kasar, ya kuma yi kira da mutanen kasar su yi shirin zaben sabbin yan majalisar dokoki nan ba da dadewa ba.
Madoros ya kara da cewa marigayi shugaba Hugo Cheves ne ya ga batar da sauye sauye na karshe a cikin kundin tsarin mulkin kasar a shekara 1999, sannan sabuwar majalisar da za'a zaba zata kara karfafa kundin tsarin mulkin ne.
Shugaba Madoros ya rattaba hannu kan wannan doka ne a jiya litinin, a dai dai lokacinda yan adawa suke jagorantar tashe tashen hankula a wasu birane a kasar.
Tuni dai yan adawar suka yi watsi da umurnin na shugaba Madoros sukakuma bayyana cewa yin hakan ya sabawa doka.