Akwai Bukatar Gudanar Da Sauye-Sauye A Majalisar Dinkin Duniya
Sakatare Janar Na MDD ya tabbata da cewa akwai bitakar gudanar da sauye sauye a Kungiyoyin kasa da kasa daga ciki har da Majalisar Dinkin Duniya
Kamfanin dillancin labaran Isna na kasar Iran ya nakalto Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a yayin da yake kan hanyarsa na zuwa birnin Landan domin halartar taron taimakawa kasar Somaliya na cewa ya zama wajibi ga kungiyoyin kasa da kasa cikin su kuwa har da MDD suka gudanar da canje canje domin tafiya da zamani.
Mista Antonio Guterres ya kara da cewa ya zama wajibi a gudanar da sauye -sauye a MDD domin karfafa sulhu da tsaro gami kare hakin bil-adama.
A wannan Alkhamis ne dai aka buda wani taro kan kasar Somaliya a birnin Landon na kasar Birtaniya kuma manufar taron shi ne nazarin hanyoyin kulla sabuwar huldar kasashen duniya da Somaliya, a fannin harakokin tsaro da tattalin arziki da nufin taimakawa kasar ci gaba kamin shekara ta 2020. Taron ya hada kan kungiyoyi kimanin 40 da suka hada da Bankin Duniya da kuma Kungiyar tarayyar kasashen larabawa.
Majalisar Dinkin Duniya na bukatar kimanin kudi da ya kai dala miliyan 900 a wannan shekara, da za'a tallafawa kasashen Afirka da ke cikin matsin rashin abin abinci da tabarbarewar tsaro. A yanzu an yi kiyasin mutane miliyan shida ke fuskatantar barazanar yunwa a kasashen Afirka, yayinda matsalar fari ya yi sanadiyar raba daruruwar 'yan Somaliya da muhallansu tun bayan barkewar matsalar a watan Nuwambar shekara ta 2016.