An Sanar Da Lokacin Yin Zaben Shugaban Kasa A Venezuela
Shugaban Kasar Venezuela ya sanar da cewa a cikin wannan shekara ta 2018 ne za a yi sabon zaben shugaban kasa.
Shugaban Kasar Venezuela ya sanar da cewa a cikin shekara ta 2018 ne za a yi sabon zaben shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarun Afeh daga Caracass ya ambato shugaba Nicholas Maduro yana cewa; A cikin 2018 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa, kuma 'yan hamayya za su sha kashi.
Maduro ya kara da cewa; A cikin kowane yanayi ne aka gudanar da zabe, to hukumar juyin juya hali ce za ta mulki kasar.
Maduro ya kuma kara da cewa; Za a yi zaben ne kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.
Venezuela tana fada da dambaruwar siyasa, inda a kowace rana 'yan hamayya masu goyon bayan Amurka su ke gudanar da Zanga-zanga da zummar kifar da gwamnati.