Yancin Mallakar Bindiga A Amurka Na Ci Gaba Da Hallaka Jama'a
Cibiyar da ke bin diddigi kan hare-haren wuce gona da iri da ake kai wa a kasar Amurka ta sanar da cewa: Hare -haren wuce gona da iri da aka kai a sassa daban daban na kasar Amurka sun yi sanadiyyar mutuwa tare da jikkatan mutane da yawansu ya kai 108 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Cibiyar da ke bin diddigi kan irin hare-haren wuce gona da iri da ake kai wa a kasar Amurka ta bayyana cewa: Harbe-harben bindiga a sassa daban daban na kasar Amurka a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sun yi sanadiyyar mutuwan mutane akalla 34 tare da jikkatan wasu 74 na daban.
Cibiyar ta kara da cewa; Mafi yawan harbe-harben sun wakana ne a jihohin Louisiana, Arkansas, Texas da Florida.
A kowace shekara dubban mutane ne suke rasa rayukansu ko jikkata a Amurka sakamakon kaddamar da hare-haren wuce gano da iri a tsakanin al'ummar kasar saboda 'yancin da suke da shi na mallakar makamai.