Oct 20, 2018 06:53 UTC
  • Mutane 2 Sun Mutu A Sanadiyyar Musayar Wuta A Yammacin Kasar Jamus

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ce; A jiya Juma'a ne aka yi musayar wuta a tsakanin 'yan sanda da wasu mutane a garin Kirchheim da yake a jahar Rhineland-Palatinate a kudu maso yammacin kasar

Tare da cewa mahukunta a yankin sun sanar da kawo karshen lamarin, sai dai ba su yi wani cikakken bayani ba akan abin da ya haddasa shi da kuma manufar maharan.

A cikin watannin bayan nan dai kasar Jamus ta rika fuskantar matsalar rashin tsaro a wasu biranenta da suka hada da hare-haren ta'addanci.

A halin da ake ciki a yanzu kasashen yammacin turai suna fuskantar barazanar tsaro saboda komawar 'yan ta'addar da suka daurewa gindi a kasar Syria.

 

Tags