Harin Bindiga Ya Hallaka Mutane 2 A Kudu Maso Yammacin Jamus
wani dan bindiga ya hallaka mutane biyu a garin Saarbrücken dake kudu maso yammacin kasar Jamus
Kafafen yada labaran kasar Jamus sun sanar da aukuwar harin bindiga a garin Saarbrücken dake kudu maso yammacin kasar a marecen jiya asabar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.
Jami'an 'yan sandar garin Saarbrücken sun sanar da cabke maharin, inda suka ce suna gudanar da bincike domin gano ko harin nada alaka da ta'addanci.
A cikin watanin baya-bayan nan kasar Jamus ta fuskanci hare-haren ta'addanci, da ya yi sanadiyar mutuwa da jikkatar mutane da dama.
A shekarun da suka gabata kasashen Yamma cikin har da kasar Jamus sun ki daukan mataki na hana 'yan ta'adda zuwa kasar Siriya domin kifar da halartacciyar gwamnatin Bashar Al-asad, a halin yanzu kuma bayan da 'yan ta'addar na ISIS suka fara komawa zuwa kasashensu, musaman ma kasashen Turai, hakan ya zamanto babbar barazana ga harakokin tsaron kasashen.