Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Mamaye Yankunan Palasdinawa
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ta kawo karshen mamaye yankunan Palasdinawa da take yi.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Palasdinu Michael Lynk ya jaddada wajabcin kawo karshen mamaye yankunan Palasdinawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take yi; yana mai fayyace cewa al'ummar Palasdinu suna rayuwa cikin mawuyacin hali a yankunansu da aka mamaye.
A tsawon kwanaki biyar kacal da Michael Lynk ya kwashe yana gudanar da ziyarar aiki a yankunan Palasdinawa da aka mamaye ya yi furuci da cewa al'ummar Palasdinu suna cikin mummunan kangi sakamakon yadda ake cin zarafinsu tare da kwace musu gidaje, gonaki, rashin 'yanci da walwala da kuma uwa uba koransu daga yankin kwata-kwata.