Ministan Harakokin Wajen Rasha : Ta'addanci Barazana Ce Ga Tsaron Duniya
Ministan tsaron kasar Rasha ya bayyana cewa ta'addanci ya kutsa cikin kasashe masu yawa kuma a yankuna daban daban musaman a yankin gabas ta tsakiya da kuma hakan ke barazana ga tsaron Duniya
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov cikin wani taron manema da labarai da suka gabatar tare da takwaransa na kasar Crotia Ivo referee Steer wannan Talata a birnin Masco ya ce da dama daga cikin kasashen Duniya da suka hada da kasashen yankin Balkans, da tsohuwar tarayyar Sobiate sun zamanto wani wuri na samar da ta'addanci da kuma sojojin haya masu dauke da makamai, inda ake hayar su suna shiga kasashen daban daban na Duniya su yi ta'addanci idan sun gama, wadanda suka tsira da rayukansu daga ciki su koma idan suka fito.
Mista Lavrov ya tabbatar da cewa dukkanin rikicin da ake fama a gabas ta tsakiya da arewacin Afrika kamar kasashen Siriya, Iraki,Libiya da kuma Yemen, akwai hanun wadannan 'yan ta'adda, kuma ya zama wajibi a gudanar da tattaunawar kasa da kasa da suka hada dukkanin bangarori da kuma kungiyoyin Addinin domin magance wannan matsala.
A bangare guda Ministan harakokin wajen na Rasha ya yi ishara kan yarjejjeniyar da kasar sa ta cimmawa da kasar Crotia wajen aiki tare da Majalisar kasashen Turai gami da Majalisar kare hakin bil-adama ta MDD domin kare hakkokin Mutane musaman ma mabiyar Addinin Kirista a yankin gabas ta tsakiya.
Rikicin kasashen Siriya da Iraki ya fara ne bayan farmakin da kungiyoyin 'yan ta'adda masu samun goyon bayan kasashen Saudiya da Amurka tare da kawansu daga ciki har da kasar Turkiya domin kawar da halarcecciyar Gwamnatin da 'yan kasashen suka zaba.