Karon Farko Dan Afrika Ya Zama Shugaban Hukumar WHO
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20666-karon_farko_dan_afrika_ya_zama_shugaban_hukumar_who
An zabi dan asalin kasar Habasha Tedros Adhanom Ghebreyesus a matsayin sabon shugaban hukumar lafiya ta duniya, wanda kunm ahakan ya kasance na farko da wani dan Afrika ya rike wannan mukami mai matukar mahimmanci a MDD.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
May 24, 2017 11:07 UTC
  • sabon shugaban hukumar WHO HOTO : AFP
    sabon shugaban hukumar WHO HOTO : AFP

An zabi dan asalin kasar Habasha Tedros Adhanom Ghebreyesus a matsayin sabon shugaban hukumar lafiya ta duniya, wanda kunm ahakan ya kasance na farko da wani dan Afrika ya rike wannan mukami mai matukar mahimmanci a MDD.

Dan Shekaru 52, Mista Adhanom ya samu wannan matsayi ne a zagaye na uku gaban abokin hammayarsa na Biritaniya David Nabarro.

Shi dai Mista Adhanom kwarare ne kan cutar zazzabin cizon sauro cewa da Malaria.

A jawabinsa bayan zabensa a matsayin sabon shugaban hukumar ta WHO ko OMS, Mista Adhanom ya yi alkawarin yin aiki tukuri ga kasashen mambobin hukumar su guda 194 akan duk abunda ya shafi shaánin kiwan lafiyar alúmma.