Biritaniya : An Cafke Mutum Uku Bayan Harin Manchester
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20668-biritaniya_an_cafke_mutum_uku_bayan_harin_manchester
Yan sanda a Biritaniya sun sanar da cafke mutane uku da ake zargi da hannu a harin kunar bakin waken birnin Manchester.
(last modified 2018-08-22T07:00:09+00:00 )
May 24, 2017 06:38 UTC
  • Biritaniya : An Cafke Mutum Uku Bayan Harin Manchester

Yan sanda a Biritaniya sun sanar da cafke mutane uku da ake zargi da hannu a harin kunar bakin waken birnin Manchester.

Ko baya ga hakan an kuma tsauraren kwararen matakai na tsaro bayan harin wanda hukumomin kasar suka danganta dana ta'addanci.

Mutane 22 ne dai suka mutu, kana wasu 59 suka jikkata sakamakon harin da aka kai a cikin daren Litinin a filin wasa na Manchester.

Kungiyar IS dai ta ce ita keda alhaki kai harin wanda shi ne mafi muni da aka taba kaiwa a wannan kasar ta Biritaniya.