Birtaniya: Musulmi Sun Nuna Alhini A Kan Harin Manchester
(last modified Thu, 25 May 2017 06:51:45 GMT )
May 25, 2017 06:51 UTC
  • Birtaniya: Musulmi Sun Nuna Alhini A Kan Harin Manchester

Musulmin kasar Birtaniya sun nuna alhininsu dangane da harin da ta’addancin da aka kai a birnin Manchester tare da kashe jama’a.

Shafin yada labarai na Fast Company ya habarta cewa, babbar cibiyar musulmin kasar Birtaniya ta fitar da bayani na yin Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a kan jama’a agarin Manchester, wanda ya yi sanadiyyar mustuwar mutane 22 tare da jikkatar wasu da dama.

Bayanin ya ce musulmin kasar Birtaniya na isar da sakon ta’aziyya da alhini ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari, tare da tabbatar musu da cewa, wanann hari ba shi da alaka da addinin muslunci, ko da kuwa wadanda suka shirya hakan sun yi da’awar cewa su musulmi ne. domin hatta musulmi ba su tsira daga ta'addancin irin wadannan mutane ba, babban misalin hakan shi ne abubuwan da suke yi a Syria da Iraki na kisan gilla a kan dubban daruruwan musulmi.

Cibiyar ta ce za ta shirya gudanar da wasu taruka a cikin biranan kasar Birtaniya domin kara wayar wa jama’a da kai hakikanin koyarwar muslunci, wadda ke yin kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna  a tsakanin ‘yan adam.