Rasha Ta Bukaci 'Yan Kasarta Su Guji Zuwa Biritaniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20736-rasha_ta_bukaci_'yan_kasarta_su_guji_zuwa_biritaniya
Rasha ta bukaci 'yan kasarta dasu guji zuwa Biritaniya saboda barazana ta'addanci a kasar bayan harin da ya yi sadadin mutuwar mutane 22 da kuma raunana wasu 75 a Manchester.
(last modified 2018-08-22T11:30:09+00:00 )
May 26, 2017 09:21 UTC
  • Rasha Ta Bukaci 'Yan Kasarta Su Guji Zuwa Biritaniya

Rasha ta bukaci 'yan kasarta dasu guji zuwa Biritaniya saboda barazana ta'addanci a kasar bayan harin da ya yi sadadin mutuwar mutane 22 da kuma raunana wasu 75 a Manchester.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar ta Rasha a Biritaniya ya fitar ta bukaci yan kasar dasu daina balaguro zuwa Biritaniya mundun dai balaguron ba na cilas ne ba.

Hakan dai a cewar sanarwar ya biyo bayan kwararen matakan da gwamnatin Biritaniyar ta dauka a baya bayan nan saboda barazanar ta'addanci.

Kawo yanzu dai 'yan sanda a kasar ta Biritaniya sun cafke mutane takwas a ci gaba da binciken da ake kan harin wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.