Gwamnatin Myanmar Ta Rufe Makarantun Musulmi A Yankin Yangun
(last modified Thu, 01 Jun 2017 06:42:06 GMT )
Jun 01, 2017 06:42 UTC
  • Gwamnatin Myanmar Ta Rufe Makarantun Musulmi A Yankin Yangun

Musulmi garin Yangun na kasar Myanmar a yammacin jiya Laraba sun gudanar da gangami domin nuna rashin amincewarsu da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na rufe musu makarantu.

Shafin yada labarai Business Standard ya bayar da rahoton cewa, mahukuntan kasar Myanmar sun dauki matakin rufe makarantun musulmin ne bayan da jagororin mabiya addinin Buda na garin suka bukaci hakan.

Musulmin birnin yangun a kasar Myanmar sun ce an rufe musu manyan makarantu guda 6, wadanda a cikinsu suke gudanar da mafi yawan ayyukan ibada a cikin watan Ramadan, kuma ba a gaya musu wani dalili na daukar wannan mataki ba, domin kuwa ba su saba wata doka ko wata kaida ba.

Sai dai a nasu bangaren 'yan sandan gwamnatin kasar Myanmar wadanda su ne suka rufe makarantun, sun bayyana cewa wannan matakin na wucin gadi, daga bisani za a baiwa musulmin damar ci gaba da gudanar da harkokinsu a cikin wadannan makarantu.