Za'a Gudanar Da Zaben Majalisar Dokokin Venezueal A Karshen Wannan Watan
Gwamnatin kasar Venezuela ta bada sanarwan cewa za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a ranar 30 ga watan yuli da muke ciki.
Majiyar muryar JMI daga Caracas babban birnin kasar Venezuela ta nakalto Tibisay Lucena shugaban hukumar zaben kasar yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa kamar yadda shugaban kasar Necolas Madoro ya yi alkawari na cewa za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a baya yanzu an tsaida lokacin gudanar da wannan zaben.
Kasar Venezuela dai ta fada cikin matsalolin saiyasa mai tsanani a cikin watannin da suka gabata wanda hakan ya tialstawa shugaba Madoros daukar matati na kawo sauye saye a kundin tsarin mulkin kasar da kuma zabar sabuwar majalisar dokoki.