Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Gobara Landan Ya Kai 17
A Birtaniya, adadin mutanen da suka mutu a mummunar gobara data kama wani bene a yammacin birnin Landan a cikin daren ranar Talata data gabata ya kai 17.
Kakakin 'yan sanda yankin, Stuart Cundy ya shaida cewa kawo yanzu an gano gawawakin mutane shida a wajen ginin wanda tuni aka tantancesu, a yayin sauren 11 da aka bayyana mutuwarsu ke har yanzu cikin benen.
Ana kuma ci gaba da nemen wasu da suka bata, kasancewar har yanzu akwai iyalan da basu da labarin sauren mutanensu.
A halinda ake ciki dai firaministar kasar Theresa May ta bukaci da a gudanar da bincike na jama'a kan wannan iftila'in.
Kawo yanzu dai babu karin bayyani akan musababbin tashin gobara, saidai masu haya benen sun danganta lamarin da rashin tsari da kuma bin ka'idodi na kiyaye gobara a benen mai hawa 24.