Za'a Kori Sojojin Kongo Daga Cikin Tawagar (MINUSCA)
A wani lokaci, yau Talata ne ake sa ran sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, zai sanar da korar wasu sojojin kasar Kongo 600 dake aiki a cikin tawagar wanzarda zamen lafiya ta (Minusca) a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.
Matakin korar sojojin dai ya biyo bayan rashin tabaka komai daga bataliyar sojojin na Kongo kan zargin dakarunta da tafka laifukan fyade.
Ko baya ga laifin fyade ana zargin sojojin na Kongo da rashin biyaya da kuma safara man fetur.
Babban kwamandan rindinar Janar Balla Keita dan asalin kasar Senegal ya ce aike da wasiku har shida a cikin wannan shekara ga bataliyar sojojin na Kongo saidai babu wani mataki da bataliyar ta dauka.
Kasar Kongo dai na da dakaru da yawan su ya kai 629 a cikin tawagar ta (Minusca) dake jibge a yankin Berberati birnin na uku mafi girma a a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.
Ko a shekara data ma MDD ta kori wasu dakarun Kongo 120, saidai babu wani canjin halaye da aka gani a wajen dakarun.