An Zargi Jami'an Gwamntin D/Congo Da Taimakawa 'Yan Tawaye
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21522-an_zargi_jami'an_gwamntin_d_congo_da_taimakawa_'yan_tawaye
Babban Kwamishinan Hukumar Kare Hakin bil-Adama na MDD ya zarki Jami'an Gwamntin Jumhoriyar Demokaradiyar Congo da taimakawa 'yan tawaye da makamai
(last modified 2018-08-22T07:00:16+00:00 )
Jun 20, 2017 13:38 UTC
  • An Zargi Jami'an Gwamntin D/Congo Da Taimakawa 'Yan Tawaye

Babban Kwamishinan Hukumar Kare Hakin bil-Adama na MDD ya zarki Jami'an Gwamntin Jumhoriyar Demokaradiyar Congo da taimakawa 'yan tawaye da makamai

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Zayed Raad Al Hussein babban kwamishinan Hukumar kare hakin bil-adama na MDD yayin da yake zarkin Gwamnatin Jumhoriyar Demokaradiyar Congo game da kafa Kungiyar 'yan tawayen Bana Mura tare da basu makamai  ya ce 'yan tawayen na Bana Mura na kai mumunan hari ne kan fararen hula na kabilun Luba da Luluwa a yankin Kasai dake tsakiyar kasar.

Al Hussein ya bayyana  hakan ne cikin wani jawabi da ya gabata wannan talala a birnin Geneva sannan ya bukaci da a dauki mataki kan wannan ta'asa da yake zarkin Gwamnatin ta Congo da aikatawa.

Domin yaki da da 'yan tawayen Kamwina Espaou, 'yan tawayen Bana Mura sun goyawa Gwmnatin ta Congo baya.

Tun daga watan Satumbar 2016 ne yankin Kasai ya zamanto wani wurin gumurzu tsakanin 'yan tawayen Kamwina Espaou da Dakarun tsaron Gwamnati tare da goyon bayan 'yan tawayen Bana Mura, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Mutane sama da dubu uku mafi yawa daga cikin su fararen hula.