Iraki: "Yan ta'addar Da'esh Masu Yawa Sun Halaka A rewacin Kasar
Jun 21, 2017 11:57 UTC
A wani hari da jami'an tsaron kasar ta Iraki su ka kai a yankin Salahuddin, sun halaka 'yan kungiyar Da'esh 12.
A wani hari da jami'an tsaron kasar ta Iraki su ka kai a yankin Salahuddin, sun halaka 'yan kungiyar Da'esh 12.
Kantoman gundumar Salahuddin, da ake arewacin Iraki, Ahamd Abdullahi al-Jaburi, ya ce; An kai harin ne a garin al-Salam mai nisan kilo mita 15 daga arewacin Biji.
A gefe daya, babban sufeton yan sandan kasar ta Iraki, " Shakir Jaudat" ya ce; A yanzu jami'an tsaro sun killace gyauron kungiyar Da'esh a cikin tsohon birnin Mosel, sai dai yan ta'addar suna amfani da mata da kananan yara a matsayin garkuwa.
Tags