Yawan Al'ummar Duniya Zai Kai Biliyan 9,8 A 2050
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto dake cewa yawan al'umma a duniya zai kai biliyan 9,8 a shekara 2050.
Rahoton wanda sashen kula da harkokin tattalin arziki da al'umma na MDD ya fitar a jiya Laraba, ya ce nan da shekaru bakwai masu zuwa Indiya za ta kasance kasa mafi yawan al'umma a duniya gaban China.
A hannu daya kuma rahoton ya ce nan da shekara 2050, Najeriya dake fuskantar bunkasuwar al'umma cikin sauri za ta iya maye gurbin Amurka a matsayi kasa ta uku mafi yawan al'umma a duniya.
Hasashen da MDD ta yi ya kuma nuna cewa, yawan al'umma a yanzu wanda ya ke a biliyan 7,6 zai kai biliyan 8,6 a shekara 2030, a yayinda a shekara 2100 zai kai 11,1.
Rahoton ya kuma ce yawan tsofafi 'yan shekara 60 zuwa sama, shi ma zai linka a tsawan shekarun, inda zai tashi daga miliyan 962 a shekara 2017 zuwa kimanin biliyan 2,1 a shekara 2050.