Kwamitin Tsaron MDD Ya Kara Wa'adin Takunkumi Kan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kara wa'adin takunkumin da ya kakaba kan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
A bayanin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Laraba yana dauke da cewa: Dukkanin mambobin kwamitin tsaron sun kada kuri'ar amincewa da daftarin kuduri mai lamba 2360 da ya nemi kara wa'adin takunkumin da aka kakaba kan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo saboda matsalolin tsaro da suke ci gaba da habaka a kasar.
Har ila yau kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya kara wa'adin aikin tawagar kwararru masu sanya ido kan tabbatar da an aiwatar da kudurin haramci da aka kakaba kan kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo zuwa ranar 1 ga watan Agustan shekara ta 2018. Kamar yadda ya yi tofin Allah tsine kan kashe mutane biyu daga cikin tawagar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya masu bincike kan laifukan cin zarafi da aka tafka a kasar.