Bukatar MDD Ga Kasar Masar Kan Zartar Da Hukuncin Kisa
Masana a hukumar kare hakkin bil'adana na Majalisar Dinkin duniya (MDD) sun bukaci gwamnatin kasar Masar ta dakatar da shirin zartar da hukuncin kisa kan mutane 6 wadanda aka kama da laifin kisan wani dansanda.
kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto hukumar kare hakkin bil'adama tana fadar haka a hiya Alhamis, ta kuma kara da cewa shaidun da aka gabatar a gaban kotu wanda ya kai ga yanke hukuncin kisa a kan wadan nan mutane bai kai shaidun da suka dace a yanke irin wannan hukuncin ba.'
Har'ila yau jami'an na hukumar kare hakkin bil'adama sun bayyana cewa an azabtar da wasu daga cikin mutanen 6 kafin su amsa cewa sune suka kashe wani jami'an dansanda a rikicin ta 2014.A shekara ta 2014 ne aka kashe daya daga cikin wadanda suke gadin alkalin da ke kula da shari'ar tsohon shugaban kasar Muhammad Mursi.