Venezuela : Maduro Ya Kori Wasu Mayan Jami'an Soji
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela, ya kori wasu mayan jami'an sojin kasar su guda hudu ciki har na jami'an 'yan sanda da ake zargi da bada umurnin yin amfani dakarfi kan masu zanga-zanga kyammar gwamnati.
Sauren mayan jami'an tsaron da aka kora sun hada dana dakarun gardi sarki dake da nauyin shawo kan masu zanga zanga dana soji da kuma na sojin ruwa.
Wannan matakin dai bai shafi babban hafsan sojin kasar ba Janar Vladimir Padrino Lopez wanda shi ne ministan tsaro kasar.
Haka zakila kuma shugaba Maduro ya sanar da shirin gwmnatin kasarsa na daukar sabbin jami'an yan sanda da sojoji 20,000 domin kara yawan jami'an tsaron kasar.
Masana al'amuran yau da kulun na ganin cewa Mista Maduro na bukatar goyan bayan mayan jami'an tsraro domin domin ci gaba da kasancewa kan madafun iko, a daidai lokacin da yan adawa na kasar ke ci gaba da yin zanga zanagr kyammar mulkinsa, baya ga tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke fama da shi.
Alkalumma shari'a daga kasar dai sun nuna cewa mutane 74 suka mutu tun bayan soma zanga-zangar kyamamr gwamnatin ta Maduro.