An Kaiwa Kotun Kolin Venezuela Hari
Gwamnatin kasar Venezuela wani jirgin yaki ya buda wuta a kan ginin Kotun kolin kasar
Kamfanin dillancin Labaran Associated Press ya nakalto Nicolas Maduro Shugaban kasar Venezuela na cewa yayin da yake gabatar da jawabi na kai tsaye a gidan Telbijin din kasar a wannan Talata, wani jirgin yaki ya buda wuta a ginin kotun kolin kasar tare kuma da jefa wata nakiya wacce ta tarwatse a harabar ginin.
Madoro ya kasar da cewa bayan kai harin a babban ginin kotun kolin, jirgin yaki ya tunkari Ma'aikatar cikin gidan inda ya ratsa ta samar Ma'aikatar.
Shugaban kasar Venezuela ya bayyana harin a matsayin wani makirci na yunkurin juyin milki da wasu marassa kishin kasa tare da hadin kai na wasu kasashen waje dake adawa da ci gaban kasar ke son yi.
Har ila yau Shugaba Maduro ya bayyana cewa Dakarun Saman kasar sun nasarar dakile wannan hari da ya kira shi a matsayin ta'addanci.
Da dama daga cikin 'yan adawa da kuma kafafen yada Labaran kasar sun dora alhakin wannan lamari da ya sanya fargaba da tsoro a tsakanin Al'ummar kasar kan Shugaba Nicolas Maduro, kuma manufar sa na yin hakan shi ne kawo karshen masu adawa da shi a cikin kasar.