An Daure Mutumin Da Ya Ci Zarafin Wata Musulma A Birtaniya
Kotun birnin New Castle a kasar Birtaniya ta daure wani mutum da ya ci zarafin wata mata musulma watanni 15 a gidan kaso tare da biyan tarar fan 140.
Shafin yada labarai na ibtimes ya bayar da rahoton cewa, mutumin mai suna Peter Scutter da shekaru 56 ya cire dan kwalin da ke kan matar musulma ne a lokacin da take yin sassaya a wata kasuwa a birnin New Castle a cikin watan Yulin 2016.
Bayan faruwar lamarin jami'an 'yan sanda sun kame shi, mutumin wanda yake fama da cutar cancer ya kasance daga cikin masu tsananin kiyayya da musulmi, inda a wasu lokuta abaya ma an taba kama shi bisa cin arafin wani musulmi.
Sai musulmar da ya ci zarafin ta ta bukaci da kada a daure shi saboda yana fama da cutar cancer, amma duk da haka alkalin kotun ya ce laifin da ya aikata ya cancanci hukuncin daurin shekara guda da watanni uku a gidan kaso.
Tun bayan faruwar lamarin, wannan mata musulma ta dauki dogon lokaci ba ta fito wajne gidanta ba, sakamakon tsoro da kuma rashin sanain tabbas a kan tsaron lafiyarta.