An Gudanar Da Zanga Zangar Kin Jinin Trump A Birnin Paris
A yayin da Shugaba Donal Trump na Amurka ke kai ziyara a kasar Faransa, Amurkawa mazauna birnin Paris sun gudanar da zanga-zangar kin jinin siyasar Shugaban na Amurka
Da safiyar jiya Ahamis ne shugaban Amurka Donald Trump ya sauka a birnin Paris na kasar Faransa, a wata ziyara da ta kwanaki uku da yake yi a kasar, inda ya gana da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.saidai a bangare guda , Amurkawa mazauna birnin Paris dauke da kyalaye na yin alawadai Shugaba Donal Trump sun gudanar da zanga-zangar kin jinin siyasar Shugaban na Amurka.
Da yammacin ranar Alhamis ce Shugaban Amurka Donald Trump da ke ziyara a kasar Faransa ya jagorancin taron manema labarai tare da takwaransa na kasar ta Faransa Emmanuel Macron. Yayin taron shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi hulda tsakanin kasashen biyu, da kuma matakan dauka a nan gaba kan batutuwa da dama.
Shugaban kasar ta Faransa ya ce yana mai cike da biyayya ga mataki shugaba Trump kan yarjejeniya yaki da dumamar yanayi ta birnin Paris, inda ya ce duk da haka za su ci gaba da tattaunawa dan ganin an samu sassauci a mataki da shugaba Trump ya dauka.
Daga nashi bangare shugaban Amurka Donald Trump ya yaba kamun luddayin shugaban na Faransa, inda ya bayyana shi a matsayin jarimin Mutum wanda zai iya tafiyar da jagorancin wannan kasa ta Faransa.