Sojojin Amurka Sun Kashe 'Yan Sanda A Afganistan
Rahotannin da ke fitowa daga yankin Kandahar na kasar Afghanistan, na cewa dakarun Amurka sun halaka jami'an 'yan sanda 16, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Su dai dakarun na Amurka sun kaddamar da lugudan wuta ne ta sama a lardin Helmand, lokacin da jami'an tsaro ke kokarin kakkabe mayakan Taliban a wani kauye da ke lardin.
Daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu har da wasu kwamadodji biyu da kuma wadanda suka jikkata. Wannan dai wani sabon koma baya ne da ake ganin Amurka ke sake samu, a aikin dawo da kwanciyar hankali a Afghanistan din.
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan kasar ta Afghanistan, Najeeb Danish, ya ce suna ci gaba da bincike kan lamarin don taimakawa iyalan wadanda harin ya ritsa da su. Shekaru biyar kenan da sojojin Amurka da Birtaniya ke jibke a lardin na Hemland.