Shugaban Venezuela Ya Mayar Da Martani Ga Barazanar Amurka
(last modified Sun, 23 Jul 2017 17:28:40 GMT )
Jul 23, 2017 17:28 UTC
  • Shugaban Venezuela Ya Mayar Da Martani Ga Barazanar Amurka

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya mayar da martani da barazanar sanya wa kasarsa takunkumin tattalin arziki da shugaban Amurka yayi yana mai cewa hakan ba zai yi tasiri ga kasar ba.

Shugaba Maduro ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar kasa ta tattalin arziki na kasar da ya kumshin ministocin gwamnati da 'yan kasuwa da sauran manyan jami'an kasar inda ya ce bisa la'akari da goyon baya da kuma alakar da ke  tsakanin kasar Venezuela da Rasha, China da Indiya don haka takunkumin ba zai yi tasiri ba.

Mr. Maduro ya kara da cewa: Kasashen Rasha, China da Indiya abokan kasuwancin kasar Venezuela ne don haka babu shakka za su goyi bayan kasar Venezuela wajen fada da wannan barazana ta Amurka.

A ranar Litinin din makon da ya wuce ne shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi barazanar cewa matukar dai kasar Venezuela ta ci gaba da shirin kafa majalisar kasar da 'yan adawa masu samun goyon bayan Amurka suke ta zanga-zanga a kai, to kuma zai kakabawa kasar takunkumi mai tsananin gaske. Gwamnatin Venezuelan ta bayyana aniyarta na gudanar da wannan zaben a ranar 30 ga wannan wata na Yuli da muke ciki.