An Kashe Wani Sojin MDD A Afrika Ta Tsakiya
Tawagar kiyaye zamen lafiya ta MDD a Afrika ta tsakiya ta sanar da mutuwar jami'inta guda da kuma raunanar wasu uku a wani harinn kauton bauna da aka kai masu a jiya Lahadi.
A cikin sanarwar data fitar tawagar ta Munusca ta ce jami'inta da ya rasa ransa dan asalin kasar Marocco ne.
An dai kaiwa ayarin motocin jami'an harin ne a yayin da suke rakiyar motocin dake dakon ruwan sha ga al'ummar dake rayuwa a kusa da tafkin yankin.
Tawagar dai ta dora alhakin kai harin ga mayakan Anti-Balaka ta galibi kiristoci, tare da mika ta'aziyarta ga iyalan mamacin da kuma gwamnatin ta Marocco.
Wannan dai na shi ne karon farko ba da ake kaiwa jami'an MDD hari a wannan kasa ta Arika ta tsakiya ba, inda ko a watan Mayun da ya gabata wani hari ya rusa da jami'an na MUNUSCA guda shida a kusa da iyaka da RD Congo.