Venezuela : An cafke Jagororin 'Yan Adawa Saboda Yunkurin Tserewa
Kotun koli a Venezuela ta ce an cafke jagoririn 'yan kasar biyu saboda yunkurin ficewa daga kasar, alhali daurin talala na a kan su.
Kotun ta ce ko baya ga yunkurin ficewa daga kasar mutanen biyu sun sabawa dokar data hana su yin bayyan ga kafofin yada labarai.
A wata sanarwar da ta fitar yau Talata kotun ta ce ta samu bayanan dake cewa mutanen biyu da suka hada da Leopoldo Lopez da Antonio Ledezma wadanda akayi daurin talala ne neman tserewa daga kasar.
Mutanen biyu dai wadanda su ne mayan jagororin 'yan adawa a wannan kasa ta Venezuella sun yi kiran jama'ar da kada su fito a zaben wakilan majalisar da shugaban kasar Nicolas Maduro ya kira ta yadda majalsar za ta rubutawa kasar sabon kundin tsarin mulki.