An bukaci Turkiya da ta daina tura makami zuwa Siriya
Rasha ta Bukaci Turkiya da ta daina tura makamai zuwa kasar Siriya
Mataimakin Ministan Harakokin wajen Rasha Gennady Gatilov cikin wata fita da ya yi tare da kamfanin dillancin labaran Bloomberg ya bayyana cewa dolle ne magabatan Ankara su daina aikewa da makamai ga 'yan ta'adda a yayin da ake shigar da kayan Agaji cikin kasar.
Har ila yau Gatilov ya aibata ruwan bama-baman da kasar Turkiya ke yi a yankunan turkawa cikin kasar ta siriya, inda ya ce dukkanin wadannan ababe da Turkiya ke yi wajibi ne ta takatar da su domin karfafa yarjejjniyar tsagaita wuta a kasar.
Kasar Rasha dai ta juma tana zarkin kasar Turkiyan da aikewa 'yan ta'adda makamai a kasar ta siriya inda gidan telbijin din kasar ya gwada faifan vidion manyan motocin Turkiya dauke da makamai suna kaiwa cikin yankunan dake kalkashin ikon 'yan ta'addar a Siriya.