Aug 13, 2017 13:44 UTC
  • Myanmar: An Hana Musulmi Zuwa Aikin Hajjin Bana

Wasu masu tsatsauran ra’ayin addinin Buda sun hana wasu daga cikin musulmin kasar Myanmar tafiya zuwa aikin haji.

Kamfanin dillancin labaran arakan ya bayar da rahoton cewa, masu tsatsauran ra’ayin addinin Buda sun hana wasu daga cikin musulmin kasar Myanmar da suka samu izinin zuwa aikin hajji tafiya zuwa aikin hajjin bana.

Rahoton ya ce dkkanin msuulmin dai sun fito ne daga garin Akyab, kuma dukkaninsu sun samu cikakkun takardun izinin zuwa aikin hajji tare da sayen tikitin jirgi, amma masu addinin Buda sun tare motocin da ke dauke da su, tare da hana su wucewa, tare da sanar da jami’an tsaro, yayin da su kuma jami’an tsaron suka tilasta musu komawa zuwa inda suka fito.

Wannan lamari ya faru ne tare da cikakkiyar masaniya daga bangaren gwamnatin kasar ta Myanmar, wadda ake zargin tana da hannu a kisan kiyashin da ake yi wa musulmin kasar kasar ‘yan kabilar Rohingya.

Har yanzu dai mahukuntan kasar ba su ce uffan kan wannan batu ba, yayin da su kum amaniyyatan ba su san makomar lamarinsu ba.

Tags