Rasha: Yarjejeniya Kan Shirin Iran Na Nukiliya Yarjejeniya Ce Ta Duniya
(last modified Sat, 19 Aug 2017 05:42:39 GMT )
Aug 19, 2017 05:42 UTC
  • Rasha: Yarjejeniya Kan Shirin Iran Na Nukiliya Yarjejeniya Ce Ta Duniya

A wani martani a kan yunkurin Amurka na rusa yarjejeniyar da aka cimmawa kan shirin Iran na nukiliya, Rasha ta bayyana cewa wannan yarjejeniya ta duniya ce baki daya, ba wata kasa guda daya ba.

A lokacin da take zantawa da manema labarai jiya a birnin Moscow na kasar Rasha, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Maria Zakharova ta bayyana cewa, Rasha za ta ci gaba da kare yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran, kuma wajibi ne dukkanin bangarorin yarjejeniya su yi aiki da ita, domin kuwa ba yarjeniya ce da ta kebanci wata kasa ba, yarjejeniya ce ta kasa da kasa.

Tun bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dare kan kujerar shugabancin kasar, yake ta shirya makarkashiya domin ganin ya rusa wannan yarjejeniya, tare da bayyanata a matsayin yarjejeniya mafi muni a tarihi.

Majalisar dinkin duniya tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA gami da kungiyar tarayyar turai, duk sun yi watsi da furucin na Donald Trump, tare da nuna cikakken goyon bayansu ga wannan yarjejeniya.