Taron Shugabannin Afirka Da Turai Kan Matsalar Kwararar Bakin Haure
A wani lokaci, a wannan Litini ce wasu shugabannin bakwai na kasashen Afirka da na Turai ke fara wani taro a birnin Paris kan matsalar kwararar bakin haure.
Shugabannin kasashen da suka samu gayyatar takwaransu na Faransa, Emmanuel Macron a wannan taron sun hada Idriss Deby Itmo na Chadi da Mahammadu Issufu na Nijar da shugaban gwamnatin hadaka ta Libiya Fayez al-Sarraj.
A bagaren Turai kuwa da akwai shugabannin kasashen Jamus cewa da Angela Merkel da shugaban gwamnatin Italiya Paolo Gentiloni da kuma na Spaniya Mariano Rajoy da kuma babbar jami'ar kula da harkokin ketare ta kungiyar tarayya turai, Federica Mogherini.
Babban manufar wannan taron shi ne jaddada goyan bayan Turai ga kasashen Chadi da Nijar da Libiya kan yadda suke tafiyarwa da kuma ciwo kan kwararar bakin haure, kamar yadda fadar shugaban kasar Faransa ta sanar.
A 'yan shekarun baya bayan kasashen Turai sun kaddamar da shirye-shirye da dama a kasashen Afirka tare da cimma yarjejeniyoyi da dama domin shawo kan matsalar ta kwararar bakin haure zuwa Turai ba bisa ka'ida ba.
Jamhuriya Nijar dake cikin kasashen Afrika dake zamen hanya ga bakin hauren na Afirka ta ce ta shawo kan matsalar a yankin Agadas dake arewacin kasar da kashi 80%.