Aug 28, 2017 12:23 UTC
  • Paparoma Ya Bukaci A Kare Hakkokin Musulmi A Myanmar

Paparoma Francis Jagoran kiristoci mabiya darikar katolika ya yi kira da a kare hakkokin musulmi 'yan kabilar rohingya a kasar Mayanmar.

Shafin yada labarai na Catholic News Agency ya bayar da rahoton cewa, Paparoma ya bayyana damuwarsa matuka dangane da halin da musulmi 'yan kabilar Rohingya suke ciki a kasar Myanmar.

Rahoton ya kara da cewa, paparoma Francis ya ce; yana bin kadun dukkanin abin da yake faruwa da 'yan uwansa musulmi a kasar Myamnar, kuma hakika halin da suke ciki yana sosa masa rai matuka, a kan haka ya jaddada kira ga dukkanin bangarori na kasa da kasa, da su sauke nauyin da ke kansu wajen kawo karshen matsalolin da musulmi 'yan kabilar Rohingya ke fama da su.

Mahukuntan kasar Myanmar dai ba su kallon musulmi 'yan kabilar Rohingya a matsayin 'yan kasa, inda suke bayyana su da cewa asalinsu baki ne da suka shigo kasar tun fiye da shekaru dari hudu da suka gaba, a kan haka ba za a taba karbarsu a matsayin 'yan kasa ba.

A cikin shekarun baya-bayan nan, musamman daga shekara ta 2012 ya zuwa yanzu, musulmin Rohingya na fuskantar kisan kiyashi daga 'yan addinin Buda masu tsatsauran ra'ayi, da kuma jami'an tsaron gwamnatin Myanmar.

Tags