Koriya Ta Arewa Ta Yi Gwajin Makamin Nukiliya Na Shida
Sep 03, 2017 06:34 UTC
Koriya ta Arewa ta sake gwajin wani makami nukiliya, wanda shi ne karo na shida, kamar yadda gwamnatin Japon ta tabbatar bayan jin girgiza kasa mai karfi maki 6,3 da sanyin safiyar yau Lahadi.
Wannan gwajin dai a cewar gwamnatin Japon zai kara rura rikicin yankin.
tun kafin hakan dama Koriya ta Arewa ta sanar da cewa ta yi nasara kera wani makamin kare dangi ko (bam hydrojen) wanda zata iya makalla shi kan sabon makaminta mai linzami dake iya kaiwa zuwa wata nahiya.
Koriya ta Arewa dai ta yi kunnan uwar shegu akan takunkumman da duniya ke kakaba mata da kuma barazana Amurka akan shirinta na makamai masu linzami.
Tags