MDD : 'Yan Rohingya 123,600 Sukayi Gudun Hijira A Bangaladash
Wasu alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya tafitar sun nuna cewa musulmin Rohingya kimanin dubu dari da ashirin da biyar ne suka tsere daga kasar Myammar domin yin gudun hijira a kasar Bangaladash.
A rahoton data fitar yau Talata MDD na fargabar kara tabarbarewar ayukan agaji, inda a cikin sa'o'i 24 aka samu 'yan gudun hijira 37,000 da suka tsallake iyaka zuwa kasar ta Bangaladash.
Jagoran ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD cewa da HCR ya ce galibin mutatnen na fama da yunwa da kishirwa, ga kuma rashin matsugunni.
Ko baya ga wannan matsala, yanayin rashin lafiyar 'yan gudun hijira na da matukar damuwa, kasancewar ana cikin lokacin damuna.
A baya bayan nan dai shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi, na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan kin tsawatawa akan cin zarafin da akewa 'yan kabilar ta Rohingha.
A wani labari kuma a gobe Laraba ne ake sa ran ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu zai kai ziyara zuwa Bangaladash kan batun 'yan gudun hijira na Rohingha.